Gobe Tinubu Zai Tafi Guinea-Bissau Halartar Taron ECOWAS
Shugaban Bola Ahmed Tinubu zai tafi kasar Guinea-Bissau a ranar Asabar don halartar taro karo na 63 na Hukumar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika (ECOWAS).
A wata sanarwar da kakakin shugaban kasan, Dele Alake, ya ce taron ana tsammanin za a gudanar da shi ne a ranar Lahadi, kuma za a tattauna muhimman batutuwan da suka shafi matsalar tsaro, sha’anin kudi, kasuwanci, tare da tattaunawa kan rahoton yanayin sauyin gwamnati a Jamhuriyar Mali, Burkina Faso da kuma Guinea.
Shugaban zai tafi da masu ba shi shawara da wasu jami’an gwamnatin Nijeriya.
Kuma zai dawo Nijeriya da zarar aka kammala taron.