Atiku Ya Caccaki Gwamnatin Najeriya Kan Rahoton Zabe Na Kungiyar Tarayyar Turai

Gidauniya Global TV and Radio > News > News > Atiku Ya Caccaki Gwamnatin Najeriya Kan Rahoton Zabe Na Kungiyar Tarayyar Turai
  • Posted by: Gidauniya FM Kano

DAGA  AISHA HUSAINI MUHAMMAD

 

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin tarayya kan yin watsi da rahoton da tawagar sa ido kan zabe ta  kungiyar tarayyar turai ta fitar kan babban zaben da aka kammala  na 2023.

Idan dai za a iya tunawa, babban jami’in sa-ido na Tarayyar Turai, Barry Andrews, ya yi ikirarin cewa kura-kuran da aka samu a zaben ya yi matukar illa ga amincin  jama’a ga hukumar zabe ta kasa INEC.

SUDAN: Likitoci sun yi gargaɗi game da ƙaruwar cutar ƙyanda a Sudan

Sai dai a wata sanarwa da ta fitar a karshen mako, gwamnatin tarayya ta yi watsi da rahoton.

Da yake mayar da martani kan kalaman gwamnatin tarayya, mai taimaka wa tsohon mataimakin shugaban kasar kan harkokin sadarwa, Phrank Shaibu, ya ce hukumar zaben ta kasa gaza wajen gudanar da ayyukanta a lokacin zaben kamar yadda kungiyar EU tayi zargi.

Author: Gidauniya FM Kano

Leave a Reply