Gwamnan Jigawa Ya Kai Ziyarar Bazata, Ya Kama Jami'an Lafiya Na Aikata Laifi

Gidauniya Global TV and Radio > News > News > Gwamnan Jigawa Ya Kai Ziyarar Bazata, Ya Kama Jami’an Lafiya Na Aikata Laifi
  • Posted by: Gidauniya FM Kano

LABARAI

Gwamnan Jigawa Ya Kai Ziyarar Bazata, Ya Kama Jami’an Lafiya Na Aikata Laifi

Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, ya kai ziyarar ba zata babban Asibitin Dutse ranar Litinin, 3 ga watan Yuni, 2023 Yayin wannan ziyara, gwamnan ya tarad da malaman lafiya suna siyar da maganin da aka tanadar na kyauta ga kananan yara Lamarin dai ya fusata gwamnan kuma ya sha alwashin cewa ba zai bar wannan laifin ya wuce haka nan ba

Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya kai ziyarar ba zata babban Asibitin Dutse, babban birnin jiha ranar Litinin, 3 ga watan Yuni, 2023.

Premium Times ta rahoto cewa yayin wannan ziyara, gwamna Namadi ya kama ma’aikatan lafiya suna siyar da magungunan da ake rabawa kananan yara kyauta.

Gwamnan Jigawa Ya Kai Ziyarar Ba Zata, Ya Kama Jami’an Lafiya Na Aikata Laifi Mai magana da yawun gwamnan, Hamisu Gumel, ya ce mai gidansa ya kira gurbataccen aikin da ya samu ma’aikatan lafiya na yi da cin amana da zagon kasa.

Gwamnan ya ce hakan ya saɓa wa tsarin gwamnatinsa na samar da magunguna ga kananan yaran da ba su cika shekaru 5 ba kyauta da kuma iyaye mata.

“Mai girma gwamna ya yi takaicin gano cewa marasa lafiya musamman kananan yaran da ba su kai shekara 5 ba sai sun sayi magani a Asbitin.”

“Wannam ya saɓa wa tsarin gwamnatin jiha na samar da kiwon lafiya kyauta ga yaran da basu wuce shekara 5 a faɗin jihar Jigawa. Kaso 70 na yaran da gwamna ya yi magana da su da mata masu shayarwa sun ce sayen magani su ke.”

“Nan take fuskar gwamna ta ɓaci kana ya ce wannan ba ƙaramin cin amana bane kuma duk mai hannu a aikata hakan zai ɗanɗana kuɗarsa,” inji Gumel.

Gumel ya ƙara da cewa mai girma gwamna bai ji daɗin yanayin da ya tsinci asibitin ba, wani ɓangaren babu wuta kuma dukka da ma’aikata da masu jinya suna zaune a duhu.

Author: Gidauniya FM Kano

Leave a Reply