Gwamnan Kano yace zaiyi dub akan albashin ma'aikatan da aka dakatar

Gidauniya Global TV and Radio > News > News > Gwamnan Kano yace zaiyi dub akan albashin ma’aikatan da aka dakatar
  • Posted by: Gidauniya FM Kano
  1. Shugaban ma’aikatan jihar Kano, Alhaji Usman Bala, da Akanta-janar na jihar, Alhaji Abdulkadir Abdulsalam tare da kwamishinan yada labarai, Alhaji Baba Halilu Dantiye, sun yunkuro domin fayyace dakatar da albashin ma’aikatan jihar 10,000.

Gidauniya ta ruwaito cewa gwamnatin jihar Kano a karkashin Abba Kabir Yusuf ta dakatar da albashin ma’aikatan gwamnati su dubu 10 wadanda gwamnatin Abdullahi Ganduje ta dauka gaf da barinta gwamnati.

Sarkin Noman Gaya Ya Nemi Gwamna Abba Ya Bullo Da Sabon Tsarin Bunkasa Noma
Ban Yi Nadamar Rusau A Kano Ba -Gwamnan Kano
Da suke magana a yayin tattaunawa da ‘yan jarida a ofishin kwamishinan yada labarai jiya, shugaban ma’aikatan ya ce, matakin da aka dauka na dakatar da biyan albashin an yi bisa dacewa da tsari da ka’idoji ma’aikata.

A cewarsa an kafa babban kwamitin da zai yi binciken kwakwaf kan sahihancin takardu da kuma matakai da hanyoyin da aka yi wajen daukan ma’aikatan aiki ‘yan watanni kalilan da karewar wa’adin mulkin tsohon gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Usman Bala ya ce, babu wani matsala za su dawo da biyan ma’aikatan da aka tantance aka tabbatar da ingancinsu musamman wadanda aka gano suna da sahihan takardu ba wai wadanda aka dauka aiki bisa alfarma ko wata manufa ta daban ba.

Author: Gidauniya FM Kano

Leave a Reply