Gwamnan Taraba Ya Rage Wa Daliban Jami’a Rabin Kudin Makaranta

Gidauniya Global TV and Radio > News > Uncategorized > Gwamnan Taraba Ya Rage Wa Daliban Jami’a Rabin Kudin Makaranta
  • Posted by: Gidauniya FM Kano

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

 

Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ya sanar da rage kudin makaranta ga daliban jami’a a Jihar da kaso 50 cikin 100 domin rage musu radadin janye tallafin man fetur.

Kakakin Gwamnan, Emmanuel Bello ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Laraba, inda ya ce ya ba da sanarwar ce a Jami’ar Jihar sannan ya jaddada muhimmancin ilimi a gwamnatinsa.

Gwamnati Ta Bayyana Yankunan Da Za A Iya Samun Ambaliyar Ruwa A Najeriya

Gwamnan ya kuma ce tuni ya jima da ayyana dokar ta-baci a bangaren ilimi.

Sanarwar ta ce, “Na damu matuka wajen samar da ilimi kyauta a matakan Firamare da Sakandare na jiharmu.

“Daliban jami’a da dama sun nuna jin dadinsu da wannan matakin, inda suka ce ragin zai bunkasa rayuwarsu sosai.

“Wasu ma daga cikin iyayen daliban wadanda ke cikin tsaka mai wuya sakamakon cire tallafin sun ce dama laluben inda za su samo kudin ya tsaya musu a rai, don haka sun ji dadi sosai.”

 

Author: Gidauniya FM Kano

Leave a Reply