DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
A ranar Talata, 4 ga watan Yulin nan a za a fara kwaso alhazan Najeriya zuwa gida.
Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da cewa ana sa ran kammala kwaso alhazan 95,000 ranar 3 ga watan Agusta.
Kwamishinan hukumar mai kula da sufurin jiragen sama, Goni Sanda ne ya sanar da haka a taron bitar aikin hajjin bana, wanda ya gudana a birnin Makkah.
Tuni dai hukumar ta fara raba wa alhazai manyan jakunkuna, gami da sanarwar fara awon kaya, wanda ta ce nan ba da jimawa ba za a rufe.
A yayin taron ne shugaban tawagar likitocin Najeriya, Dokta Usman Galadima ya sanar da rasuwar alhazan Najeriya hudu a ranar Arafa, wanda hakan ya kara yawan alhazan da suka rasu zuwa 13