SERAP ta buƙaci Tinubu da ya bayyana yadda aka kashe biliyan 400 ta tallafin man fetur da ya ce an cire

Gidauniya Global TV and Radio > News > News > SERAP ta buƙaci Tinubu da ya bayyana yadda aka kashe biliyan 400 ta tallafin man fetur da ya ce an cire
  • Posted by: Gidauniya FM Kano

Kungiyar Rajin Kare Tattalin Arziki (SERAP) ta bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi amfani da ikonsa na shugabanci ya gaggawa buga bayanan yadda aka kashe Naira biliyan 400 ya zuwa yanzu da aka ce an same su sakamakon cire tallafin man fetur.

SERAP ta bukace shi da ya ba da cikakkun bayanai kan tsare-tsare na yadda kudaden da ake kashewa a baya daga cire tallafin man fetur, da suka hada da wasu ayyuka na musamman da za a kashe kudaden a kansu, da kuma hanyoyin da aka bi don tabbatar da cewa ba a yi sama-da-faɗi ko karkatar da kuɗaɗen zuwa aljihunan wasu shafaffu da mai ba.

Rahotanni sun bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta tara Naira biliyan 400 a cikin makonni hudu bayan aiwatar da manufar cire tallafin man fetur.

A cikin wasika mai dauke da kwanan watan 1 ga watan Yuli 2023 mai dauke da sa hannun mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, kungiyar ta ce: “Gwamnatin ku na da alhakin da ya rataya a wuyanta na ganin an kashe kudaden da aka tara daga cire tallafin man fetur ne kawai don amfanin talakawa miliyan 137. ‘Yan Najeriya da ke da alhakin a kai.”

SERAP ta ce, “Hana cin hanci da rashawa wajen kashe kudaden da ake kashewa daga cire tallafin man fetur da kuma hanawa da magance kalubalen da ake samu daga amfani da kudaden wani abu ne da zai amfanar da jama’a.”

A cewar SERAP, “Yan Najeriya na da ‘yancin sanin yadda ake kashe kudaden. Buga cikakkun bayanai game da kashe kudaden da aka tara, zai samar da gaskiya da rikon amana, da kuma rage illar cin hanci da rashawa wajen kashe kudaden.

Author: Gidauniya FM Kano

Leave a Reply