‘Yan bindiga a jihar Filato ta arewacin Najeriya sun kashe akalla mutane 9 tare da kone gidaje yayin wani hari da suka kai yankin Sabon Gari a karamar hukumar Mangu ta jahar
Harin wanda tuni mahukuntan jihar suka tabbatar da faruwarsa shi ne na baya-baya cikin jerin hare-haren da jihar ke gani masu alaka da addinin da kuma kabilanci wadanda ke ci gaba da tsananta a sassan jihar wadda ta yi kaurin suna da tashe-tashen hankula da kuma rikicin addini.
Jerry Datim guda cikin shugabannin yankin da aka kai harin na daren jiya asabar, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya yau lahadi cewa da tsakaddare ne batagarin rike da bindigogi suka farwa al’ummar yankin na Sabon gari tare da kone gidaje 6 da tarin dukuyoyin jama’a.
A cewar Mr Datim wanda mamba ne na kungiyar tabbatar da zaman lafiyar jihohin tsakiyar arewa, zuwa yanzu sun yi nasarar gano gawarwakin mutane 9 sai dai akwai tarin wasu da suka bace tun bayan kai harin na daren asabar.
Mr Datim ya bukaci runduna ta musamman da aka samar don tabbatar da tsaron jihar wato Operation Rainbow ta kara kaimi wajen dakile makamantan hare-haren