Za A Fara Daukar Fasinjoji Kyauta A Motocin ‘Kanawa Bus’

Gidauniya Global TV and Radio > News > News > Za A Fara Daukar Fasinjoji Kyauta A Motocin ‘Kanawa Bus’
  • Posted by: Gidauniya FM Kano

 

 

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarnin fara jigilar fasinjoji kyauta a Motocin Kanawa Bus da gwamnatin jihar ta samar daga ranar Litinin.

 

Sanarwar hakan ta bulla ne ta shafin Facebook na babban mai ba shi shawara a bangaren kafafen sada zumunta Abubakar Aminu Ibrahim, dauke da sa hannun Injiniya Rabiu Sulaiman Bichi, inda ya ce matakin ya biyo bayan rashin tsabar kudi da ake fama da shi a kasar.

 

 

Wannan mataki na zuwa ne bayan dokar sauya takardun N1,000, N500 da kuma N200 ta haifar da karancin tsabar kudi a hannun ’yan Najeriya.

 

Tun a watan Nuwamba ne dai da Gwamnatin Jihar Kano ta kirkiri dokar hana baburan a daidaita Sahu bin wasu manyan hanyoyi, ta kuma samar da manyan motocin da kuma kanana na taksi don jigilar fasinjoji.

 

 

Hukumar Kula da Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) ce ta fitar da sanarwar, tare da barazanar daukar mataki kan duk wanda ya saba dokar, sai dai zanga-zanga da koke-koken al’umma ya sanya dokar ba ta dore ba.

 

 

Author: Gidauniya FM Kano

Leave a Reply

1 Comment